1 Timothy 5

1Kada ka tsauta wa dattijo. Sai dai ka gargade shi kamar mahaifi. Ka gargadi samari kamar ‘yan’uwa. 2Gargadi dattawa mata kamar iyaye mata, ‘yan mata kamar ‘yan’uwa mata cikin dukkan tsarki.

3Ka girmama gwamraye, gwamraye na gaske. 4Amma gwamruwar da take da ‘ya’ya ko jikoki, bari su fara nuna bangirma cikin danginsu. Bari su sakawa iya-yensu, domin Allah yana jin dadin haka.

5Amma gwamruwa ta gaske da ke ita kadai, ta kafa begenta ga Allah. Kullum tana tsananta yin roke-roke da addu‘o’i dare da rana. 6Amma, mace mai son zaman annashuwa ta riga ta mutu, ko da shike tana raye.

7Kuma ka yi wa’azin wadannan al’amura donsu zama marasa abin zargi. 8Amma idan mutum bai iya biyan bukatun ‘yan’uwansa ba, musamman iyalin gidansa, ya musunci bangaskiya, kuma gara marar bi da shi.

9Bari a lisafta mace gwamruwa idan ba ta kasa shekara sittin ba, matar miji daya. 10A san ta da kyawawan ayyuka, ko ta kula da ‘ya’yanta, ko tana mai karbar baki, ko mai wanke kafafun masubi, ko mai taimakon wadanda ake tsanantawa, mai naciya ga kowanne kyakkyawan aiki.

11Amma game da gwamraye masu kuruciya, kada a sa su cikin lissafi. Domin idan suka fada cikin sha’awoyin jiki da ke gaba da Almasihu, sukan so su yi aure. 12Ta wannan hanya ce sun tara wa kansu tsarguwa saboda sun tada alkawarinsu na fari. 13Sun saba da halin ragwanci, suna yawo gida gida. Ba zama raggwaye kawai su ka yi ba. Amma sun zama magulmata, masu shishshigi, masu karambani. Suna fadin abin da bai dace ba.

14Saboda haka ina so gwamraye masu kuruciya su yi aure, su haifi ‘ya’ya, su kula da gida, domin kada a ba magabci zarafin zargin mu ga aikata mugunta. 15Domin wadansu sun rigaya sun kauce zuwa ga bin shaidan. 16Idan wata mace mai bada gaskiya tana da gwamraye, bari ta taimakesu, don kada a nawaita wa Ikilisiya, domin Ikilisiya ta iya taimakon gwamraye na gaske.

17Dattawa wadanda suke mulki da kyau sun cancanci girmamawa ninki biyu, musamman wadanda suke aiki da kalma da kuma koyarwa. 18Gama nassi ya ce, “Kada a sa takunkumi a bakin takarkari lokacin da yake sussukar hatsi,” kuma “Ma’aikaci ya cancanci a biya shi hakinsa.”

19Kada ka karbi zargi game da dattijo sai shaidu sun kai biyu ko uku. 20Ka tsauta wa masu zunubi gaban kowa domin sauran su ji tsoro.

21Na umarce ka a gaban Allah, da Almasihu Yesu, da zababbun mala’iku ka kiyaye ka’idodin nan ban da hassada kuma kada ka yi komai da nuna bambanci. 22Kada ka yi garajen dibiya wa kowa hannuwa. Kada ka yi tarayya cikin zunuban wani. Ka tsare kanka da tsabta.

23Kada ka ci gaba da shan ruwa. Amma, maimakon haka ka sha ruwan inabi kadan saboda cikinka da yawan rashin lafiyarka. 24Zunuban wadansu mutane a bayyane suke, sun yi gaba da su cikin hukunci. Amma wadansu zunubansu na bin baya. Haka kuma, wadansu kyawawan ayyukansu a bayyane suke, amma wadan sun ma ba su boyuwa.

25

Copyright information for HauULB